24/07/2026
BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA DR. JAMIL MUHAMMAD SADIS.
Assalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.
Bayan gaisuwar Musulunci, ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Malam lafiya, Ya tsawaita rayuwarsa cikin imani da ayyukan alheri, Ya kuma ci gaba da sanya albarka a cikin iliminsa da aikinsa.
A gaskiya, duk lokacin da na tuna irin baiwar ilimin Alƙur'ani da Allah Ya h**e wa Malam, musamman a fannin Qirā'āt, zuciyata tana cika da farin ciki da alfahari kasancewar Malam ɗaya ne daga cikin fitattun 'ya'yan Najeriya da Allah Ya ɗaukaka da wannan ni'ima.
Allah Ya ƙara wa Malam ɗaukaka.malam kaine ka fara PhD a Qismin Qiraat a Daliban Kaduna dama Nigeria baki daya a Jamiar Islamiyya ta Madina ga shi Allah Ya ba ka baiwar iya isar da ilmi cikin hikima, natsuwa da ƙwarewa.
Sai dai kuma, zuciyata tana jin zafi idan na tuna cewa babu wani tsayayyen majalisi na musamman da Malam ya keɓe domin koyar da wannan ilmi mai daraja ga masu neman ilmi a ƙasarmu.
A yau akwai ɗimbin matasa masu sha'awar koyon Qirā'āt,
Saboda haka, cikin cikakkiyar girmamawa da ladabi, ina roƙon Malam da ya keɓe wani lokaci na musamman domin koyar da ɗaliban ilmi. Matsayi ko nauyin aiki bai taɓa hana yada ilimin Alƙur'ani ba, musamman idan aka yi la'akari da girman ladan da ke cikin koyar da Littafin Allah.
Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Mafificinku shi ne wanda ya koyi Alƙur'ani kuma ya koyar da shi."
(Sahihul Bukhari)
Hakika, akwai ɗalibai da dama waɗanda ba su san irin baiwar da Allah Ya yi wa Malam a fannin Qirā'āt ba. Idan aka buɗe wannan ƙofa, za ta zama babban alheri ga al'umma, kuma za ta taimaka wajen samar da ƙwararrun makaranta a wannan fanni a Najeriya.
Ilimin Qira'at ilimi ne mai sarkakiya, mai yawa, wanda yana buqatan zaratan mallamai irin su Dr, kuma shine fannin da Dr. Jameel Muhammad Sadis yayi Degree na ɗaya har zuwa na uku akanshi, Lallai nasan abinda Dr zai bayar ba duk 'da ba, kuma ga dalibai masu yawan gaske suna kishin ruwan abin.
Don Allah, Malam, a karɓi wannan shawara da kyakkyawar zuciya. Muna roƙon Allah Ya sanya ta ta zama alheri, Ya ci gaba da kare Malam, Ya ƙara masa ilmi mai amfani, Ya kuma sanya shi cikin bayinsa masu hidimar Alƙur'ani har ƙarshen rayuwa.
Ku tayani Isarwa.
Wassalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.
✍️Ministan musabaqa
24/07/2026