27/02/2026
AL'UMMAR GARIN BIU BA ZASU TABA MANTAWA BA
Cikin daren Lahadi, misalin ƙarfe bakwai na dare 15 ga Maris 2011, aka salwantar da rayuwar babban malaminmu, Sheikh Ibrahim Ahmad Gomari, Malamin Sunnah, mai gabatar da tafsirin Al-Qur’ani, jagora ga al’umma a Darul Hadith Galdimare Tafsir Center, Biu😭
An sha yi masa barazanar cewa za'a kashe shi, Mutane sunyi ta bashi shawarar ya gudu domin kada a halaka shi, Amma sai ya amsa da kalmar da ta girgiza zukata: “Babu inda ba'a mutuwa.” A wannan daren na 15 March 2011 aka harbe shi a kirjinsa da kansa, aka kashe shi ba tare da tausayi ba.
A watan Ramadana, babu wani wuri a Biu da jama’a ke cincirindo don sauraron tafsirin Alqur'ani mai girma kamar inda yake zaune yana fassara Littafin Allah. Murya tayi shiru Al'umma su taru domin sauraron sa
Wallahi, an zalunce mu zalunci mai tsanani. An raba mu da malami, jagora. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Duk wanda ya tuna wannan ranar musavmman mu yan garin Biu zuciyarsa ba za ta hana zubar da hawaye ba.
Abdullahi Sautussunnah Biu✍