13/06/2026
WASIKAR MAI UNGUWAR MU ZUWA GA 'YAN UNGUWAR MU
OFFISHIN DAGACHIN GOBIRAWA
Assalamu alaikum bayan gaisuwa mai yawa
A madadin dagatai da masu unguwanni da limamai, muna fadakarwa ga iyayen yara musamman su tsawatarwa da yayansu su guji zuwa kallon fadan daba.
Daga yanzu duk yaron da aka k**a a cikin rigimar daba za'a dau matakin shari'a.
Suna kara jawa iyaye kunne akan yayansu masu zuwa kallo yan babu ruwana, cewa idan ana wannan rigima to kowa ya killace dansaa gida saboda gudun karsu hana ma'aikata aikinsu.
Saboda gudun tsautsayi ya fada wa wadanda ba ruwansu, domin ma'aikata zasu iya amfani da tiyagas, domin kwantar da tarzoma, kokuma wajen gudu da mota ko bullet ya samu yaro, saboda haka ake jawo hankalin iyaye su kula da yayansu musamman da daddare, ana bawa iyaye shawara cewa su killace yayansu daga bayan isha'imusamman wadanda s**a kai shekaru 18 zuwa kasa.
Sannan kuma duk wanda aka k**a dansa kar yaje Police Station idan kuma yaje to shima hukuma zata hukuntashi, domin abar hukuma tayi aikinta.
Domin haka ake kara son iyaye su jawa Yayansu kunne akan zuwa kallon fadan daba.
IN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA
VILLAGE HEAD
Musa Isah Muhammad